Daniel 11:39 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai kai wa kagarai mafi ƙarfi hari da taimakon baƙon allah zai kuma girmama waɗanda suka yarda da shi zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ ڨُوثٜىٰ وُرَارٜىٰ مَاسُ كَتَنْ‌غَ مَڢِے ڧَرْڢِے دَ تَيْمَكُوانْ اللَّهْ‌نَّنْ نَوَتَ ڧَسَا؞ وَطَنْدَ سُكَ يَرْدَ دَشِ، ذَيْبَاسُ غِرْمَ، يَكُمَبَاسُ مَڟَيِنْ شُوغَبَنِّ عَكَنْ مُتَنٜىٰ دَيَوَ، يَرَبَ مُسُ ڧَسَا تَذَمَ لَادَنْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai tasar wa kagara mafi ƙarfi da taimakon baƙon gunki. Waɗanda suka yarda da shi, zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.