Daniel 11:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Wani daga cikin zuriyarta zai taso yă ɗauki matsayinta. Zai kai wa sojojin sarkin Arewa hari yă kuma shiga kagararsa; zai yi yaƙi da su yă kuma yi nasara.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ ݣُونَكِنَّنْ، وَنِ دَغَ ثِكِنْ ذُرِيَرْتَ ذَيْ تَاسُواْ؞ ذَيْ كَيْ وَ سُواْجُواْجِ نَسَرْكِنْ أَرٜىٰوَ يَاڧِ، حَرْ ذَيْ شِغَ وُرَارٜىٰنْسُ مَاسُ كَتَنْغَ، يَثِ نَصَرَا عَكَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.