Daniel 12:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَيْ كَمَنِّنْ طَنْ أَدَمْ يَثِيغَبَدَ مَغَنَ يَثٜىٰ «أَوَنَّنْ لُواْكَثِ مِيكَآءِيلُ، مَلاَىِٕكَ شُوغَبَنْ جَمَعَرْكَ ذَيْ تَاشِ يَطَوْكِ مَتَاكِ؞ ذَاعَيِ ݣُونَكِنْ عَذَابَ إِرِ وَدَّ بَعَتَٻَيِبَ تُنْدَ عَكَيِ دُونِيَا؞ عَمَّا أَ لُواْكَثِنْ، ذَاعَ كُٻُتَرْ دَ جَمَعَرْكَ، دُكْ وَنْدَ عَكَ رُبُوتَ سُونَنْسَ عَثِكِنْ لِتَّڢِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A wannan lokaci Mika'ilu babban shugaba wanda yake lura da jama'arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama'arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi.