Daniel 2:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki suka ce, “Babu wani mutum a duniyan nan da zai iya yin abin da sarki yake nema! Babu wani sarki mai daraja da girma wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya ga masu sihiri ko masu dabo ko masanan taurari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً ڠُونَيٜىٰنْ ڟَاڢِنْ سُكَ أَمْسَ وَسَرْكِے سُكَثٜىٰ «أَ دُكَنْ ڢَاطِنْ دُونِيَرْ نَنْ، بَابُوَنِ وَنْدَ ذَيْ عِيَيِنْ أَبِنْدَ سَرْكِے يَكٜىٰثٜىٰ عَيِ؞ حَڧِيڧَ، بَا وَنِ سَرْكِے وَنْدَ يَتَٻَ يِنْ إِرِنْ وَنَّنْ تَمْبَيَ أَوُرِنْ مَيْ سِحِرِ، كُواْ مَيْ دَبُواْ، كُواْ وَنِ ڠُونِنْ ڟَاڢِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Kaldiyawa suka amsa wa sarki, suka ce, “Ba wani mahaluki a duniya wanda zai iya biyan wannan bukata ta sarki, gama ba wani sarki wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya a wurin mai sihiri, ko mai dabo, ko Bakaldiye.