Daniel 2:45 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا مَعَنَرْ مَڢَرْكِنْ دُوڟٜىٰنْدَ كَغَنِ؞ عَثِكِنْ مَڢَرْكِنْ كَغَ دُوڟٜىٰ يَٻَرْكٜىٰ دَغَ بَبَّنْ تُدُ، كُمَ بَ دَ حَنُّنْ طَنْ أَدَمْ بَ، حَرْ يَڢَرْڢَشٜىٰ بَڧِنْ ڧَرْڢٜىٰنْ دَ تَغُلَّرْ دَ لَكَرْ دَ أَظُرْڢَرْ دَ ظِينَارِيَرْ؞ تُواْ، اللَّهْ مَطَوْكَكِ يَنَ سَنَرْوَ سَرْكِے أَبِنْدَ ذَيْ ڢَرُ نَنْ غَبَ كٜىٰنَنْ؞ مَڢَرْكِنْ تَبَّتَاثّٜىٰنٜىٰ، مَعَنَرْسَ كُمَ غَسْكِيَثٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kamar yadda ka ga an gutsuro dutse ba da hannun ɗan adam ba, ya kuwa ragargaje baƙin ƙarfen, da tagullar, da yumɓun, da azurfar, da zinariyar, Allah Maɗaukaki ya sanar wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin tabbatacce ne, fassarar kuma gaskiya ce.”