Daniel 2:48 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے يَبَا دَانِيٜىٰلْ غِرْمَ مَيْ يَوَ دَ مَنْيَ مَنْيَنْ ݣَوْتَيْ مَاسُيَوَ؞ يَنَطَشِ مَيْمُلْكِ بِسَ دُكَنْ يَنْكِنْ بَابِيلَ؞ يَكُمَ نَطَشِ شُوغَبَنْ دُكَنْ مَاسُ حِكِمَ نَ بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila.