Daniel 2:49 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَانِيٜىٰلْ يَضُواْڧِ سَرْكِے أَمَدَدِنْ أَبُواْكَنْسَ، سَرْكِے كُوَ يَنَطَ شَدْرَكْ دَ مٜىٰشَكْ دَ أَبٜىٰدْنٜىٰغُواْ سُذَمَ مَاسُ كُلَ دَ أَلْعَمُرَنْ يَنْكِنْ بَابِيلَ؞ عَمَّا دَانِيٜىٰلْ يَكَسَنْثٜىٰ عَثِكِنْ غِدَنْ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daniyel kuwa ya roƙi sarki ya naɗa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego su zama masu kula da harkokin lardin Babila, amma Daniyel yana fādar sarki.