Daniel 3:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya aika a kira hakimai da wakilai da gwamnoni da mashawarta, da ma’aji, da alƙalai, da marubutan kotu, da dukan sauran ma’aikatan yankunan, suka hallara domin a rusuna wa wannan siffar da ya kafa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَعَيْكَ عَكِرَوُاْ هَكِمَنْ يَنْكُنَ دَ مَاسُ مَڟَيِ دَ ڠُومْنُواْنِ دَسُو مَاسُ بَادَ شَوَرَا دَسُو مَعَجِ دَ أَلْڧَلَيْ دَ مَاسُ شَرِيعَ دَ دُكَنْ دَتَّاوَنْ يَنْكُنَ سُذُواْ، دُواْمِنْ سُكَسَنْثٜىٰ عَبِكٍ كٜىٰٻٜىٰوَرْ غُنْكِنْ ظِينَارِيَ وَنْدَ شِ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَكَڢَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya aika a kirawo su hakimai, da wakilai, da su muƙaddasai, da 'yan majalisa, da su ma'aji, da alƙalai, da masu mulki, da dukan ma'aikatan larduna, su zo, su halarci bikin keɓewar gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.