Daniel 3:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً هَكِمَنْ يَنْكُنَ دَ مَاسُ مَڟَيِ دَ ڠُومْنُواْنِ دَ مَاسُبَا سَرْكِے شَوَرَا، دُكَنْسُ سُكَ تَارُ كٜىٰوَيٜىٰ دَ مُتَنٜىٰنَّنْ؞ سُكَغَ لَلَّيْ وُتَرْ بَتَيِ وَجِكُنَنْ مُتَنٜىٰنَّنْ كُواْمٜىٰبَ؞ غَاشِنْ كَوُنَنْسُ مَا كُواْ طَيَ بَيْ ثِوُتَبَ، كَايَنْ جِكِنْسُ مَا بَسُثِ وُتَابَ، كُواْ وَرِنْ وُتَا مَا بَابُ أَجِكِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan su hakimai, da wakilai, da muƙaddasai, da manyan 'yan majalisa suka taru, suka ga lalle wutar ba ta yi wa jikunan mutanen nan lahani ba, gashin kawunansu bai ƙuna ba, tufafinsu ba su ci wuta ba, ko warin wuta babu a jikinsu.