Daniel 3:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَ عُمَرْتَرْكُ ثٜىٰوَ سَعَدَّ كُكَجِ ڧَارَرْ ڧَهُواْ دَ سَرٜىٰوَ دَ غَرَايَ دَ مُواْلُواْ دَ كَثَوْ كَثَوْ دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ أَبِنْ كَطٜىٰ كَطٜىٰ دَ بُوشٜىٰ بُوشٜىٰ، سَيْ كُڢَاطِ ڧَسَا، كُيِ سُجَّدَ غَ غُنْكِنْ ظِينَارِيَرْ نَنْ وَنْدَ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَكَڢَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
cewa sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi, ku yi sujada ga gunkin zinariyan nan da sarki Nebukadnezzar ya kafa.