Daniel 3:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ حَكَ، سَعَدَّ دُكَنْ ڧَبِيلُ دَ أَلْعُمَّيْ دَ مَاسُ يَرٜىٰ دَبَمْ دَبَمْ سُكَجِ ڧَارَرْ ڧَهُواْ دَ سَرٜىٰوَ دَ غَرَايَ دَ مُواْلُواْ دَ كَثَوْ كَثَوْ دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ أَبِنْ كَطٜىٰ كَطٜىٰ دَ بُوشٜىٰ بُوشٜىٰ، سَيْ سُكَ ڢَاطِ ڧَسَا، سُكَيِ سُجَّدَ غَ غُنْكِنْ ظِينَارِيَرْ نَنْ وَنْدَ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَكَڢَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa.