Daniel 4:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Wannan shi ne mafarkin da ni, Nebukadnezzar, na yi. Yanzu Belteshazar, sai ka faɗa mini abin da yake nufi, domin babu wani a cikin masu hikima a mulkina da ya iya fassara mini shi. Amma za ka iya, domin ruhun alloli masu tsarki yana a bisanka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَثٜىٰ «وَنَّنْ شِينٜىٰ مَڢَرْكِنْ دَنِے نَا يِ؞ كَيْ كُمَ بٜىٰلْتٜىٰشَظَّرْ، سَيْ كَڢَطَا مِنِ مَعَنَرْسَ، غَمَا دُكَنْ مَاسُ حِكِمَ نَثِكِنْ مُلْكِنَ بَسُ عِيَ ڢَطَا مِنِ مَعَنَرْسَبَ؞ عَمَّا كَيْ ذَاكَ عِيَ، غَمَا رُوحٌ أَلُّواْلِ مَاسُ ڟَرْكِے يَنَ ثِكِنْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“ ‘Mafarkin da ni sarki Nebukadnezzar na yi ke nan. Kai Belteshazzar kuma, sai ka faɗa mini ma'anarsa, domin dukan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗar mini ma'anar, amma kai ka iya, gama ruhun alloli tsarkaka yana cikinka.’ ”