Daniel 4:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ya sarki ka ga ɗan saƙon mai tsarkin nan, yana saukowa daga sama yana cewa, ‘A sare itacen a hallaka shi, amma a bar kututturensa daure da ƙarfe da tagulla, a bar shi can a ɗanyar ciyawar filaye, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namun jeji har shekara bakwai.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«يَا سَرْكِے، سَعَدَّ كَكٜىٰ كَلُّواْ، سَيْغَا وَنِ مَلاَىِٕكَ مَيْ ڟَرْكِے، طَنْ سِنْتِرِ يَنَ سَوْكُواْوَ دَغَ سَمَ؞ يَنَ ثٜىٰوَ ‹أَ سَارٜىٰ إِتَاثٜىٰنَّنْ، أَ هَلَّكَ شِ، عَمَّا عَبَرْ تُوشٜىٰنْ دَ سَيْوُاْيِنْسَ ثِكِنْ ڧَسَا؞ أَ طَطَّوْرٜىٰ دَ سَرْڧَرْ بَڧِنْ ڧَرْڢٜىٰ دَ تَغُلَّ، عَبَرْ شِ أَطَنْيَرْ ثِيَوَ؞ بَرِ رَٻَ تَيِ تَجِڧٜىٰشِ، يَذَوْنَ تَرٜىٰدَ نَمُواْمِنْ دَاجِ حَرْ ڟَوُانْ لُواْكَثِ بَݣَويْ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.