Daniel 4:34 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada. Mulkinsa dawwammamen mulki ne; sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَڧَرْشٜىٰنْ ݣُونَكِنَّنْ، سَيْ نِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ، نَطَغَ عِدُواْ سَمَ، سَيْ حَنْكَلِنَ يَكُواْمُواْ مِنِ؞ نَكُوَ غِرْمَمَ مَڢِے طَوْكَكَ ، نَيَبٜىٰشِ، نَغِرْمَمَشِ، شِے وَنْدَ يَكٜىٰ رَايٜىٰ حَرْ أَبَدَا؞ غَمَا مُلْكِنْسَ مُلْكِنٜىٰ نَهَرْ أَبَدَا، مُلْكِنْسَ دَغَ ڟَارَا ذُوَا ڟَارَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.