Daniel 4:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ بَايَ سَيْ وَنِ سَوْرَيِ مَيْ سُونَ دَانِيٜىٰلْ يَشِغُواْ؞ وَنَّنْ دَانِيٜىٰلْ كُوَ أَنْكُمَ سَنْ شِ دَ سُونَ بٜىٰلْتٜىٰشَظَّرْ، وَتُواْ سُونَنْ اللَّهْنَ؞ شِے مُتُمْ نٜىٰ ثِكٜىٰ دَ رُوحٌ أَلُّواْلِ مَاسُ ڟَرْكِے؞ نَا كُوَ ڢَطَا مَسَ مَڢَرْكِنْدَ نَيِ، نَثٜىٰ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga baya sai Daniyel wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, wato irin sunan allahna, yana kuwa da ruhun alloli tsarkaka, ya shigo wurina. Na kuwa faɗa masa mafarkin, na ce,