Daniel 5:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ مُتُمْ شِينٜىٰ دَانِيٜىٰلْ وَنْدَ بَابَنْكَ يَثَنْجَ مَسَ سُونَ ذُوَا بٜىٰلْتٜىٰشَظَّرْ؞ شِ مُتُمْ نٜىٰ مَيْ ثِكٜىٰ دَ رُوحٌ بَنْ مَامَاكِ دَ سَنِ دَ بَسِيرَ؞ وَنَّنْ يَسَا يَ عِيَ بَيَّنَ مَعَنَرْ مَڢَرْكَيْ دَ تَكَثِثِ كَثِثِ، يَكُمَ عِيَ وَرْوَارٜىٰ أَلْعَمُرَ مَاسُ وُيَ؞ بَرِ إِنْ سَرْكِے يَيَرْدَ، يَعَيْكَ عَكِرَوُاْ دَانِيٜىٰلْ دُواْمِنْ يَبَادَ مَعَنَرْ وَنَّنْ أَبِنْدَ كَغَنِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yana da ruhun nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma'anar.”