Daniel 5:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَانِيٜىٰلْ كُوَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ وَ سَرْكِے، «رَنْكَيَدَطٜىٰ! ذَاكَ عِيَ رِڧٜىٰ ݣَوْتَرْكَ، كُواْ كَبَا وَنِ؞ دُكْدَهَكَ ذَنْ كَرَنْتَ وَسَرْكِے رُبُوتُنْ، إِنْكُمَ بَيَّنَ مَسَ مَعَنَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daniyel kuwa ya amsa, ya ce wa sarki, “Riƙe kyautarka, ka ba wani duk da haka zan karanta wa sarki rubutun, in kuma bayyana masa ma'anarsa.