Daniel 5:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَكٜىٰ شَنْ ضُوً إِنَبِے، سَيْ بٜىٰلْشَظَّرْ يَعُمَرْتَ عَكَٰوُاْ ݣُوڢُنَ نَظِينَارِيَ دَ نَأَظُرْڢَا دُواْمِنْ شِے دَ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْسَ دَ مَاتَنْسَ دَ مَاتَانْدَ يَأَجِيٜىٰ، سُشَا دَغَ ثِكِنْسُ؞ وَطَنَّنْ ݣُوڢُنَ كُوَ سُنَ ثِكِنْ كَايَيَّكِنْ دَ بَابَنْسَ نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَݣُوشٜىٰ دَغَ هَيْكَلِ أَ عُرُوشَلِيمَ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Belshazzar ya kurɓa ruwan inabin, sai ya umarta a kawo tasoshi na zinariya da na azurfa waɗanda Nebukadnezzar ubansa ya kwaso daga Haikali a Urushalima, domin sarki, da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa su sha ruwan inabi da su.