Daniel 6:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَثٜىٰ وَسَرْكِے «رَنْكَيَدَطٜىٰ يَا سَرْكِے! دَانِيٜىٰلْ طِنَّنْ، وَنْدَ يَكٜىٰ طَيَ دَغَ ثِكِنْ وَطَنْدَ عَكَ كَٰوُاْ بَوْتَادَغَ ڧَسَرْ يَهُودَ، بَيْ كُلَ دَكَيْ بَ، بَلّٜىٰ ڢَا عَثٜىٰ يَكُلَ دَ دُواْكَرْدَ كَكَڢَ؞ عَمَّا يَنَ تَيِنْ أَدُّعُواْعِنْ ضُواْڧٜىٰ ضُواْڧٜىٰنْسَ سَوْ عُكُ كُواْوَثٜىٰ رَانَ غَ اللَّهْ نْسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”