Daniel 6:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے يَعُمَرْتَ عَكَٰوُاْ دَانِيٜىٰلْ، عَكَ كَٰوُاْشِ عَكَ تُورَشِ أَرَامِنْ ذَاكُواْكِ؞ سَرْكِے كُمَ يَثٜىٰ وَ دَانِيٜىٰلْ «بَرِ اللَّهْ نْكَ وَنْدَ كَكٜىٰ بَوْتَا مَسَ كُلُّمْ يَثٜىٰثٜىٰكَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.”