Daniel 6:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَنَطَ شُوغَبَنِّ غُدَا عُكُ سُلُورَ دَ هَكِمَنْ يَنْكُنَنَّنْ؞ دَانِيٜىٰلْ كُوَ طَيَ نٜىٰ عَثِكِنْ شُوغَبَنِّ عُكُنَّنْ؞ أَغَرٜىٰسُنٜىٰ دُكَنْ هَكِمَنْ يَنْكُنَنَّنْ سُكَنْ بَادَ رَهُواْتُوانْ عَيْكِنْسُ دُواْمِنْ كَدَ سَرْكِے يَرَسَ وَنِ أَبُ دَغَ مُلْكِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome.