Daniel 6:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَثِكَ دَ مُرْنَ ڨُورَيْ، يَعُمَرْتَ أَ ڢِتُواْ دَ دَانِيٜىٰلْ دَغَ رَامِنْ؞ سَيْ عَكَ ڢِتُواْ دَ دَانِيٜىٰلْ دَغَ رَامِنْ، عَكَ غَ بَا وَنِ أَبِنْدَ يَتَٻَ جِكِنْسَ سَبُواْدَ يَدُواْغَرَ غَ اللَّهْ نْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki ya cika da murna ƙwarai, ya umarta a fito da Daniyel daga kogon. Sai aka fito da Daniyel daga kogon, aka ga ba wani lahani a jikinsa saboda ya dogara ga Allahnsa.