Daniel 6:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarki ya umarta, a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ’ya’yansu, da matansu cikin ramin zakoki. Kafin ma su kai ƙurewar ramin, sai zakoki suka hallaka su suka yayyage su, suka yi kaca-kaca da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے يَعُمَرْتَ عَكَٰوُاْ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَيِ وَ دَانِيٜىٰلْ ڧُلّٜىٰ ڧُلّٜىٰنَّنْ؞ سَيْ يَعُمَرْتَ عَتُورَسُ دَ یَیَنْسُ دَ مَاتَنْسُ ثِكِنْ رَامِنْ ذَاكُواْكِنْ؞ تُنْ بَسُ كَيْ غِدَنْ رَامِنْبَ، سَيْ ذَاكُواْكِ سُكَ ثَڢْكٜىٰسُ دَغَ سَمَ، سُكَ كَكَّرْيٜىٰ دُكَنْ ڧَسُسُوَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da 'ya'yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.