Daniel 6:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ أَنْغَانٜىٰ ثٜىٰوَ دَانِيٜىٰلْ دَبَمْ نٜىٰ دَ سَوْرَنْ شُوغَبَنِّ دَ هَكِمَنْ يَنْكُنَ، غَمَا أَݣَويْ رُوحٌ بَنْ مَامَاكِ عَثِكِنْسَ؞ سَيْ سَرْكِے يَشِرْيَ يَدَّ ذَيْبَاشِ مَڟَيِنْ إِيكُواْ عَكَنْ دُكَنْ مُلْكٍ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Daniyel ya shahara fiye da sauran shugabannin, da su muƙaddasan, domin yana da nagarin ruhu a cikinsa. Sarki kuwa ya shirya ya gabatar da shi kan dukan mulkin.