Daniel 6:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ شُوغَبَنِّنْ مُلْكِ دَ مَاسُ مَڟَيِ دَ هَكِمَنْ يَنْكُنَ دَ مَاسُ بَادَ شَوَرَا دَ ڠُومْنُواْنِ سُنْ يَرْدَ ثٜىٰوَ يَا كَمَاتَ سَرْكِے يَكَڢَ دُواْكَا، يَكُمَ تَبَّتَرْ أَنْبِتَ؞ رَنْكَيَدَطٜىٰ سَرْكِے! دُواْكَرْ دَ ذَاكَ كَڢَ عِتَثٜىٰ عَثِكِنْ ݣُونَ تَلَتِنَّنْ غَبَ أَغَرٜىٰكَ نٜىٰ كَطَيْ ذَاعَيِ أَدُّعَ؞ دُكْ وَنْدَ يَيِ أَدُّعَ غَ وَنِ مُتُمْ كُواْ وَنِ اللَّهْ، إِنْ بَ غَرٜىٰكَبَ، يَا سَرْكِے، ذَاعَ جٜىٰڢَرْ دَشِ عَثِكِنْ رَامِنْ ذَاكُواْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan shugabannin ƙasar da masu mulki da muƙaddasai, da 'yan majalisa, da wakilai, sun tsai da shawara, cewa ya kamata sarki ya kafa doka, ya yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, sai a tura shi cikin kogon zakoki.