Daniel 7:20 โ Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma so in gane game da ฦahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ฦahon nan da ya fito, wanda aka tumษuke ฦahoni uku a gabansa, ฦahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma.
Hausa Arabic 2020 (ุงููุชููููุฑูุชู ุฏู ุงูููููุจูุงููุง)
ููููู
ูุณููุงู ุงููููุณููู ู
ูุนูููุฑู ฺงููููุงููู ุบููุงูู
ู ุนูููููุชู ุฏู ุทููู ฺงููููุงููุฏู ูููปูููููุงูุ ููููุฏู ุนููู ุชูู
ููปูููููฐ ฺงููููุงููู ุนููู ุงููุบูุจูููุณูุ ุงูููู ุณููุงู ุงููููุณููู ู
ูุนูููุฑู ฺงููููุงูููููู ููููุฏู ููููููฐุฏู ุงููุฏูุงููู ุฏู ุจูุงูููู ุฏูููููููฐ ฺขูุทููู ู
ููููููู ู
ูุบูููโุบููููู ุทูุบู ููููุ ููููุฏู ุงููุบูููููู ุบูุฑูู
ูููุณู ฺููขู ููุณูููุฑูููุ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na kuma so in san ma'anar ฦahoninta goma, da ษaya ฦahon wanda ya tsiro, wanda aka tumษuke ฦahoni uku a gabansa. ฦahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.