Daniel 7:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«غَا بَيَانِنْ دَيَبَانِ؞ يَثٜىٰ، ‹دَبَّ تَهُطُ تَݣُوتَنْتَا مُلْكِ نَهُطُ عَدُونِيَا، وَنْدَ ذَيْ بَمْبَنْتَ دَ دُكَنْ سَوْرَنْ مُلْكُواْكِنْ؞ ذَيْثِنْيٜىٰ دُونِيَا دُكَ، يَتَتَّاكٜىٰتَ، يَڢَرْڢَشٜىٰتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.