Daniel 7:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَيْ كُمَ غَ وَتَ دَبَّ تَبِيُ وَدَّ تَكٜىٰدَ كَمَنِّنْ بٜىٰيَرْ؞ غٜىٰڢٜىٰ طَيَ نَجِكِنْتَ يَطَغَ سَمَ ڢِيٜىٰدَ طَيَنْ؞ تَنَ رِڧٜىٰ دَ هَڧَرْڧَرِ عُكُ أَ هَڧُواْرَنْتَ؞ سَيْ عَكَثٜىٰ مَتَ، ‹تَاشِ، كِثِكَ ثِكِنْكِ دَ نَامَ!›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sai kuma ga dabba ta biyu mai kama da beyar. Gefe guda na jikinta ya ɗara ɗaya. Tana riƙe da haƙarƙari uku a haƙoranta! Sai aka ce mata, ‘Tashi ki cika cikinki da nama.’