Daniel 8:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na ɗaga ido, a gabana kuwa sai ga rago mai ƙahoni biyu, yana tsaye a gefen mashigin kogin, ƙahonin kuma suna da tsawo. Ɗaya daga cikin ƙahonin ya fi ɗayan tsawo. Wanda ya fi tsawon shi ne ya tsiro daga baya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ نَطَغَ عِدُواْ، سَيْ نَغَ ضَغُواْ أَڟَيٜىٰ عَبَاكِنْ رَاڢِنْ؞ يَنَ دَ ڧَهُواْنِ بِيُ دُواْغَيٜىٰ، عَمَّا طَيَ يَڢِ طَيَنْ ڟَوُاْ؞ وَنْدَ يَڢِ دُواْغُواْ شِينٜىٰ يَڟِرُواْ دَغَ بَايَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da na ta da idanuna, sai na ga rago a tsaye a gāɓar kogin. Yana da ƙaho biyu dogaye, amma ɗaya ya ɗara ɗaya tsawo. Wanda ya ɗara tsawon shi ne ya tsiro daga baya.