Daniel 8:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, ya kai wa ragon hari. Ya kakkarya ƙahoninsa nan biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, bai iya kāre kansa daga bunsurun ba. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَغَ يَذُواْ كُسَدَ ضَغُوانْ دَ ڢُشِے مَيْ ڟَنَنِ ڨُورَيْ؞ سَيْ يَكَيْوَ ضَغُوانْ هَرِ، حَرْ يَكَكَّرْيَ ڧَهُواْنِنْسَ نَنْ بِيُ؞ ضَغُوانْ بَيْ عِيَ ڟَيَاوَا يَيِ غَابَادَ بُنْسُرُنْبَ؞ بُنْسُرُنْ يَبُغٜىٰشِ ڧَسَا يَتَتَّاكٜىٰشِ؞ بَاوَنْدَ يَ عِيَ كُٻُتَرْدَ ضَغُوانْ دَغَ بُنْسُرُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, sai ya gabza wa ragon karo. Ya kakkarya ƙahonin nan nasa biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, ba ya iya kare kansa daga bunsurun. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.