Daniel 8:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga cikin ɗayansu kuma wani ƙaramin ƙaho ya fito, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai zuwa kudu da kuma gabas da wajen Kyakkyawar Ƙasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ ثِكِنْسُ سَيْ وَنِ ڧَرَمِنْ ڧَهُواْ كُمَ يَڟِرُواْ، يَيِ غِرْمَ يَبَظُو كُواْعِنَ؞ إِيكُوانْسَ يَكَيْ حَرْ ذُوَا وَجٜىٰنْ غَبَسْ دَ وَجٜىٰنْ كُدُ دَ وَجٜىٰنْ ڧَسَا مَيْ دَرَجَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wani ƙaramin ƙaho kuma ya tsiro daga cikin ɗayansu, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai. Ya nuna ikonsa wajen gabas, da wajen kudu, da wajen ƙasa mai albarka.