Daniel 9:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے دَانِيٜىٰلْ نَبِنْثِكَ لِتَّتَّڢَيْ مَاسُ ڟَرْكِے، سَيْ نَغَانٜىٰ ثٜىٰوَ ذَاعَيِ شٜىٰكَرَا سَبَعِنْ عُرُوشَلِيمَ تَنَ ذَمَنْ كُڢَيْ، بِسَغَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ذُوَاغَ أَنَّبِے إِرْمِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
a wannan shekara ta sarautarsa ni Daniyel, ina nazarin littattafai, sai na ga labarin shekara saba'in ɗin nan da Ubangiji ya faɗa wa annabi Irmiya. Su ne yawan shekarun da Urushalima za ta yi tana zaman kango.