Deuteronomy 1:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَوَنَّنْ لُواْكَثِ نَغَرْغَطِے مَاسُ شَرِيعَرْكُ نَثٜىٰ، ‹كُسَوْرَرِ ضِكِثِنْ دَيَكٜىٰ ڟَكَانِنْ جُونَنْكُ، كُيِ شَرِيعَرْ غَسْكِيَ ڟَكَانِنْ مُتُمْ دَ طَنْعُوَنْسَ، كُواْ طَنْ ڧَسَا نٜىٰ كُواْ بَڧُوانْ دَيَكٜىٰ ذَمَ عَثِكِنْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A wannan lokaci kuma na umarci shugabanninku na ce, ‘Ku yi adalci cikin shari'a tsakanin 'yan'uwanku, tsakanin mutum da ɗan'uwansa, ko kuma da baren da yake zaune tare da shi.