Deuteronomy 12:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
to, sai ku lura, kada ku jarrabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku, kada ku tambayi kome game da allolinsu, kuna cewa, “Yaya waɗannan al’ummai suke bauta wa allolinsu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَيِ حَكَ، سَيْ كُلُورَ ڢَا، كَدَ سُذَمَ مُكُ تَرْكُواْ كُبِے هَنْيُواْيِنْسُ بَايَنْدَ أَنْكَوَرْ دَسُو دَغَ غَبَنْكُ؞ كَدَ كُنٜىٰمِ سَنِنْ وَنِ أَبُ غَمٜىٰدَ أَلُّواْلِنْسُ كُنَ ثٜىٰوَ ‹يَيَ وَطَنَّنْ أَلْعُمَّيْ سُكٜىٰيِ وَ أَلُّواْلِنْسُ سُجَّدَ؟ مُو مَا ذَامُيِ كَمَرْ يَدَّ سُكٜىٰيِ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
to, sai ku lura, kada ku jarabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku! Kada ku tambayi labarin kome na gumakansu, ku ce, ‘Ƙaƙa waɗannan al'ummai suka bauta wa gumakansu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.’