Deuteronomy 13:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا أَنَّبِنَّنْ كُواْ مَيْ مَڢَرْكِنَّنْ، ذَاعَ كَشٜىٰشِ، سَبُواْدَ يَكُواْيَرْ دَ تَاوَيٜىٰ عَكَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ، وَنْدَ يَڢِتَرْ دَكُو دَغَ ڧَسَرْ مَصَرْ، وَنْدَ كُمَ يَڢَنْشٜىٰكُ دَغَ غِدَنْ بَوْتَا؞ إِرِنْ مُتَنٜىٰنَّنْ مُوغَيٜىٰنٜىٰ وَطَنْدَ سُكٜىٰسُواْ كُكَوْثٜىٰ دَغَ حَنْيَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَعُمَرْثٜىٰكُ كُبِے؞ تَهَكَ ذَاكُ كَوَرْدَ مُغُنْتَادَغَ ثِكِنْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.