Deuteronomy 14:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku ci zakkar hatsinku, da na sabon ruwan inabinku, da na manku, da kuma na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, don ku koyi girmama Ubangiji Allahnku kullum.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ، أَوُرِنْ دَ ذَيْ ذَاٻَا دُواْمِنْ عَيِ سُجَّدَ دَ سُونَنْسَ نٜىٰ، ذَاكُثِ زَكَّ تَسَابُوانْ حَڟِنْكُ دَ تَضُوً إِنَبِنْكُ مَيْ ذَاڧِ دَ تَمَنْكُ دَ تَیَیَنْ ڢَارِ نَغَرْكٜىٰنْ شَانُنْكُ دَ نَتُمَكِنْكُ دَ أَوَكِنْكُ، دُواْمِنْ كُكُواْيَ يَدَّ ذَاكُيِ تَڢِيَ ثِكِنْ ڟُواْرُوانْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ حَرْ أَبَدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.