Deuteronomy 14:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كُكَشٜىٰ كُطِنْ عَكَنْ دُكْ أَبِنْدَ كُكٜىٰسُواْ، وَتُواْ كُواْ شَانُو نٜىٰ، كُواْ تُمَكِ، كُواْ ضُوً إِنَبِے، كُواْ أَبِنْ سَا بُغُوَ، كُواْ دَيْ دُكْ أَبِنْدَ رَنْكُ يَكٜىٰسُواْ؞ أَوُرِنْ نٜىٰ ذَاكُيِ بِكِ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ، كُو دَ عِيَلَنْ غِدَنْكُ كُيِ مُرْنَ تَرٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ku kashe kuɗin a kan duk abin da kuke so, ko sa ne, ko tunkiya, ko ruwan inabi, ko abin sha mai gafi, ko dai duk irin abin da ranku yake so. Nan za ku yi liyafa a gaban Ubangiji Allahnku, ku yi murna tare da iyalan gidanku.