Deuteronomy 14:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma, cikin waɗanda suke sāke tona abin da suka riga suka haɗiye ɗin, ko suke da rababben kofato, ba za ku ci raƙumi, zomo ko rema ba. Ko da yake suna sāke tona abin da suka riga suka haɗiye, suna kuma da rababben kofato, su ɗin marar tsarki ne gare ku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دُكْدَهَكَ، عَثِكِنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ تُڧَرْ عَبِنْثِ عَبَاكِ دَ وَطَنْدَ تَڢِنْ ڧَڢَاڢُنْتَ سُنْ رَبُ بِيُ، بَذَاكُثِ رَاڧُمِ دَ ذُواْمُواْ دَ رٜىٰمَبَ؞ كُواْدَيَكٜىٰ سُنَ تُڧَرْ عَبِنْثِ عَبَاكِ، تَڢِنْ ڧَڢَاڢُنْسُ بَسُ رَبُ بِيُبَ؞ دُواْمِنْ حَكَ أَبِنْ ڧَظَنْتَا نٜىٰ أَغَرٜىٰكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma duk da haka cikin waɗanda suke tuƙa, da waɗanda suke da rababben kofato ba za ku ci raƙumi, da zomo, da rema ba, ko da yake suna tuƙa, amma ba su da rababben kofato. Haram ne su a gare ku.