Deuteronomy 15:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku keɓe wa Ubangiji Allahnku kowane ɗan fari na garkenku na shanu, da na tumaki. Kada ku sa ɗan fari na shanunku aiki, kada kuma ku aske gashin ɗan fari na tumakinku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«ذَاكُ كٜىٰٻٜىٰ غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ دُكَنْ یَیَنْ ڢَارِ مَظَا نَغَرْكٜىٰنْكُ نَشَانُو دَ نَتُمَكِ دَ نَأَوَكِ؞ بَذَاكُيِ عَيْكِنْ نُواْمَ دَ طَنْ ڢَارِ نَشَانُنْكُ بَ، بَذَاكُ كُمَ أَسْكٜىٰ غَاشِنْ طَنْ ڢَارِ نَتُنْكِيَرْكُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sai ku keɓe wa Ubangiji Allahnku dukan 'yan fari maza waɗanda aka haifa muku daga cikin garkenku na shanu, da na tumaki, da na awaki. Kada ku yi aiki da ɗan farin shanunku, kada kuma ku sausayi ɗan farin tunkiyarku.