Deuteronomy 16:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kwana bakwai za ku yi shagalin Bikin ga Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa. Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan girbinku da kuma cikin dukan aikin hannuwanku, farin cikinku kuwa zai cika.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ݣُونَ بَݣَويْ ذَاكُيِ بِكٍ سُجَّدَ غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ أَوُرِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَذَاٻَا دُواْمِنْ عَيِ مَسَ سُجَّدَ، غَمَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ ذَيْ أَلْبَرْكَثٜىٰكُ ثِكِنْ دُكَنْ أَمْڢَانِنْ غُواْنَكِنْكُ دَ دُكَنْ أَيُّكَنْ حَنُّوَنْكُ، كُمَ لَلَّيْ ذَاكُيِ مُرْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku kiyaye idin ga Ubangiji Allahnku har kwana bakwai a inda Ubangiji zai zaɓa, gama Ubangiji Allahnku zai yalwata dukan amfanin gonakinku, da dukan ayyukan hannunku don ku cika da murna.