Deuteronomy 16:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada a iske yisti a cikin mallakarku a dukan ƙasarku har kwana bakwai. Kada ku bar wani nama na hadayar da kuka yi a yammancin ranar farko, yă kwana har safe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاعَ سَامِ يِسْتِ أَدُكَنْ يَنْكِنْكُ بَ حَرْ ݣُونَكِے بَݣَويْ؞ بَذَاكُ كُمَ بَرْ نَامَنْ هَدَايَرْدَ كُكَ يَنْكَ دَ يَمَّ أَ رَانَ تَڢَارِ يَݣُونَ حَرْ وَايٜىٰوَرْ غَرِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada a iske yisti a ƙasarku duka har kwana bakwai. Kada kuma ku ajiye naman hadayar da kuka miƙa da yamma a rana ta fari ya kwana har safiya.