Deuteronomy 17:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ku tabbata kun naɗa sarki a kanku wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa ne. Dole yă zama daga cikin ’yan’uwanku. Kada ku sa baƙo a kanku, wanda ba mutumin Isra’ila ɗan’uwanku ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، سَيْ كُتَبَّتَا كُنَطَ وَكَنْكُ سَرْكِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ ذَيْ ذَاٻَا؞ كُنَطَ وَنِ دَغَ ثِكِنْ یَنْعُوَنْكُ يَذَمَ سَرْكِنْكُ؞ بَذَاكُ نَطَ بَڧُواْ يَذَمَ سَرْكِے عَكَنْكُبَ، وَنْدَ شِے بَدَغَ ثِكِنْ جَمَعَرْكُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama'arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan'uwanku ba.