Deuteronomy 17:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In aka kawo ƙarar da yake da wuya sosai ga alƙali a kotunanku, ko wadda aka zub da jini ne, ko ta faɗa ce, ko kuwa ta wadda aka ci mutunci ce, ku kai su wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ عَكَ كَٰوُاْ مُكُ شَرِيعَ مَيْ وُيَرْ يَنْكٜىٰوَ، كُواْ تَكِسَنْ كَيْ ثٜىٰ، كُواْ تَكَشٜىٰ وَنِ بَ دَ غَنْغَنْبَ، كُواْ تَثِنْ مُتُنْثِ نٜىٰ، كُواْ تَوَنِ إِرِنْ ضِكِثِنْ دَ ذَيْ كَيْكُ شَرِيعَنٜىٰ، سَيْ كُتَڢِے وُرِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ ذَيْ ذَاٻَا دُواْمِنْ عَيِ مَسَ سُجَّدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Idan aka kawo muku shari'a mai wuyar yankewa a ɗakin shari'arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari'a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.