Deuteronomy 17:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku je wurin firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, ga kuma alƙalin wanda yake mulki a lokacin. Ku bincika daga gare su, za su kuwa ba da hukunci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كُكَيْ مَغَنَرْ وُرِنْ ڢِرِسْتُواْثِے، وَتُواْ ذُرِيَرْ لَوِ دَ مَيْ شَرِيعَ وَنْدَ يَكٜىٰ عَيْكِ أَ لُواْكَثِنْ؞ كُتَمْبَيٜىٰسُ، ذَاسُ كُوَ يَنْكٜىٰ شَرِيعَرْ دَ تَدَاثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku kai maganar wurin Lawiyawan da suke firistoci, ko kuma a wurin alƙalin da yake aiki a lokacin. Za ku tambaye su, za su faɗa muku yadda za a yanke shari'a.