Deuteronomy 19:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shaidar mutum guda ba tă isa a tabbatar cewa mutum yana da laifi game da laifin da ake tuhumarsa ba, ko kuwa a kan wani laifin da ake zaginsa da aikata ba. Dole a tabbata da batun ta bakin shaidu biyu, ko uku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«شَيْدَرْ مُتُمْ طَيَ، بَذَاتَ إِسَ عَبَا وَنِ لَيْڢِے كُواْ عَتَبَّتَرْ دَ ذُنُوبِ بَ، سَيْدَيْ أَجِ تَبَاكِنْ شَيْدُ بِيُ كُواْ عُكُ كَاڢِنْ مَغَنَ ذَاتَ تَبَّتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Shaidar mutum ɗaya ba za ta isa a tabbatar, cewa mutum ya yi laifi ba, sai a ji shaidar mutum biyu ko uku, kafin a tabbatar da laifin mutum.