Deuteronomy 2:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan rana zan fara sa tsoro da fargabanku a kan dukan al’ummai, a ƙarƙashin sama. Za su ji labarinku, za su yi rawan jiki, su kuma damu saboda ku.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ يَوْ ذَنْ ڢَارَ سَا ڟُواْرُوانْكُ يَڢَاطُواْ عَكَنْ دُكَنْ ڧَبِيلُ كُواْعِنَ عَڧَرْڧَشِنْ سَمَ، ذَاسُ ڢِرْغِتَ؞ سَعَدَّ سُكَجِ لَابَرِنْكُ، ذَاسُيِ ضَوَرْ جِكِے، سُدَامُ ڨُورَيْ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”