Deuteronomy 21:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
kada ku bar jikinsa a kan itacen yă kwana. Ku tabbata kun binne shi a ranar, domin duk wanda aka rataye a kan itace la’ananne ne ga Allah. Kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاعَبَرْ غَاوَرْ جِكِنْسَ تَݣُونَ عَكَنْ إِتَاثٜىٰنْبَ؞ ذَاعَبِنّٜىٰشِ أَ رَانَرْ، غَمَا دُكْ وَنْدَ عَكَ رَاتَيٜىٰشِ لَعَنَنّٜىٰ نٜىٰ غَ اللَّهْ ؞ كُبِنّٜىٰشِ دُواْمِنْ كَدَ كُڧَظَنْتَرْدَ ڧَسَرْدَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَكٜىٰ بَاكُ غَادُواْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”