Deuteronomy 21:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Karɓi wannan kafara saboda mutanenka Isra’ila, wanda ka fansar, ya Ubangiji, kada kuma ka ɗaura wa mutanenka alhakin jinin mutumin nan marar laifi.” Za a kuwa yi kafarar zub da jinin da aka yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا يَهْوٜىٰهْ ، كَغَاڢَرْتَا وَمُتَنٜىٰنْكَ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنْدَ كَڢَنْسَ، كُمَ كَدَ كَبَرْ أَلْحَكِنْ جِنِنْ مَرَرْ لَيْڢِے يَذَوْنَ عَثِكِنْ مُتَنٜىٰنْكَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞› ذَاعَكُوَ غَاڢَرْتَا مُسُ أَلْحَكِنْ وَنَّنْ جِنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama'arka, Isra'ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama'arka, Isra'ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.’