Deuteronomy 22:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In kuka ga jakin ɗan’uwanku, ko saniyarsa ya fāɗi a kan hanya, kada ku ƙyale shi. Ku taimaka, ku tā da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ كَا غَا جَاكِ كُواْ بِجِمِ نَمَڨُوبْثِنْكَ يَڢَاطِ عَكَنْ حَنْيَ، بَذَاكَ ڨَلٜىٰشِ بَ، يَا كَمَاتَ كَتَيْمَكٜىٰشِ كَطَغَ شِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi.