Deuteronomy 24:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku zalunci ɗan ƙodago matalauci da mabukaci, ko da shi ɗan’uwanku ne mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a cikin garuruwanku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بَذَاكَ ثُوثِ لٜىٰبُرَ وَنْدَ يَكٜىٰ مَتَلَوْثِ كُمَ مَيْ بُڧَاتَ، كُواْ شِے طَنْعُوَنْكَ مُتُمِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ نٜىٰ، كُواْ شِے بَڧُواْ نٜىٰ وَنْدَ يَكٜىٰ ذَمَ عَثِكِنْ وَنِ غَرِ عَڧَسَرْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Kada ku zalunci ɗan ƙodago wanda yake matalauci, ko shi danginku ne, ko kuwa baƙon da yake zaune a garuruwan ƙasarku.